Mutane kusan dubu 500 suka shiga zanga-zangan na yau a wurare dubu daya a sassan kasar kamar yadda Ministan harkokin cikin gida Christophe Castaner ya sanar.
Wasu bayanai na nuna an sami rasa rai na wata mace dake kan hanyar kai ‘yarta asibiti a lokacin da masu bore suka kewaye motar ta aka rika dukan motar.
Masu zanga-zangan na adawa ne da matakan da shugaban kasar Emmanuel Macron ke dauka na rage gurbacewar yanayi dake haifar da tsadan man fetur .
Ministan ya bayyana cewa ana daukan matakai don tabbatar da ba’a sami mummunar yamutsi ba ko rufe hanyoyi da zai iya kai ga rudani.